BAN YI TUNANI BA 16 to 20

••••••••••❤❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤••••••••••
••••••••••❤••••••••••


*BAN YI TUNANI BA*


® *{P M L W}*
_pure moment of life writers_
```(we don't just entertain and educate we also touch the hearts of the readers)```



Beebahwadata.blogspot.com



     *Written by*
```Beebah wadata```



_in dedication to *Mss Zuhura* ILYSM dear_


*16 to 20*

Sai da suka hau titi sannan ya d'aura hannunsa akan cinyarta same tym yana kallonta

"Haba Muneef miye haka,idan mukayi accident pha" ta fad'a tana tur'e hannunsa

"Nothing will happened da yarda Allah ba inda bana Iya xuwa haka,driving da hannu daya".

"Naji duk da haka dai"
Dai dai sun kawo kofar gidan hon sukayi mai gadi yaxo ya bude


Hunaida da ke falo zauna ai tanaji hon tace

"Mami kamar motan uncle naji?".

"Ba mamaki shine tinda abba yana abuja".

"Bari naje na dubo"
Tana mik'ewa su kuma suna yin sallama kenan,da gudu tayi huggin din Husna.

"Ke karki balla min mata" Muneef ya Fada

"Tohh.....uncle ina nayi girman da zan balla ta"

"Koma dai minene ki dinga yi a hankali''

"Eh yeee toh sarkin rashin kunya,Allah ya kawo mu zamani,Ba'a yi ba sai bana" Aunty Bilkisu ta Fada

Ya'r dariya yayi "kin ga laifina Aunty ni kadai nasan kwakwan da naci kafin na same ta" ya k'arashe maganar yana kallon Husna....

"Aunty ina wuni'' Husna ta Fada
Sai a lokacin shima Muneef ya gaisheta

Sai da ka gama masifar sannan zaka gaida ni,kar kasa na rik'e yata nace an fasa auren......Lapia lau Husna ya kwanan gida?"

"Lapia lau" kawai tace
''Ayi hakuri toh kar a rabani da Hussynah"ya fada tare dayin fuskar tausayi

"Hunaida je ki d'auko musu abinci kitchen".
'Toh' tace ta mik'e

"Amm Aunty daman na xo na gaya maki gobe pha zanyi tafia zuwa Thailand ni aka zaba zanyi representing company".yayi maganar cikin damuwa

"Allah ya taimaka,ya kuma bada sa'a.....toh nace basu San jiya kayi aure bane".

"Ameen,sun Sani mana tinda sun tafi dauren aure".

" Idan kaje yaushe zaka dawo?''

"A month zanyi"

"Ita kuma Husna pha?".

"Nan zata zauna har na dawo''.

"Toh Allah yasa haka shi yafi zama alkhari".
"Ameen" suka ce su dukka

"Uncle na gama had'a abinci yana dinning".

"Sai anyi sallah za mu ci ba ki ji kiran sallah bane,Yarinya sai kace kurma".

Aunty Husna ke yanxu zaki ci?......Kai kuma idan dan nine kar k......

Bakinta ya bige
"Mara kunya kawai"
Yayi hanya fita falon

"Bari muyi sallah kawai tashi muje muyi alwala"Husna ta Fad'a,tare da jan hannun hunaida suka shiga ciki,daman aunty ta dad'e da tashi gurin,dakin hunaida suka shiga,Nan sukayi sallah,bayan sun gama suka je dakin aunty Bilkisu
  Bayan sun gaisheta ne take tambayar Husna ko tana da wani matsala ne?.
   Ta shaida mata bata da ko d'aya.....
Yar fira suka taba akayi kiran isha'i,suka fita  suyi sallah.
Muneef ma bai dawo ba sai da yayi sallah isha
Abinci suka ci saanan suka fara fira

  " wai aunty nikam yaushe Khalid zai dawo ne?" Muneef ya tambaya?

"Ce mani yayi next week zasu gama exams dasun gama zai dawo".

"Yeehh..Dan uwana ya kusa dawowa".Hunaida tace

"kenan ba zamu hadu ba,lokacin da zai zo na wuce"

"Ai kodai,Aunty hussy bake sanshi ba koh"?

" Eh yaran gidan uncle Lawan kawai na sani"

"Za ki San shi idan ya dawo,tinda kenan nan gidan"

"Ku tashi pha Ku tafi kar dare yayi maku".

Muneef ya kalle agogon hannunsa
"Kai 15min to  10  tashi muje hussy"

"Kaje kawai gobe ka kawo man kayana kafin ka tashi tafiya". Tayi mai murmushi

"Tashi muje karki batamin lokaci mana".

"Tashi kije gobe dai komi kwakwar mutum kina nan shiko yana can" Hunaida tace

"Ke kin rainani ko sai na fasa wannan shegen bakin naki"

Dariya kawai tayi tare da yi masa gwalo
"Aunty hussy tashi na raka ki mota koh d'aki nah zaki je"

"Eh muje dakin".
Har suna mike zasu tafi Muneef ya rik'ota

" ki zo muje plx " Ta kanne mashi ido
Dariya ya basu irin yadda yayi saurin riqota,suka tuntsire da dariya

"Ku tashi Ku tafi" Aunty Bilkisu tace

Saanan suka yi masu sai da safe suka wuce,har sun kai kofan fita falon Hunaida tace

"Uncle ko nazo mu tafi tare na kwana acan"
Hara'ra kawai ya banko mata sukayi gaba....

Suna Isa kowa ya wuce nashi dakin
D'akin Husna na shige na ganta ta fito wanka d'aure da towel tana tsane jikinta kallo na bita dashi gaskiya kam Allah yayi mace anan,Ga kyau,gashi,diri..gaban mirror naga ta zauna ta shafa wani lotion,rigar dake kan gado ta dauko ta saka Iya karta gwiwa,wutan d'akin ta kashe ta jawo kofar ta rufe,wani d'aki ta bude nima na bita ciki
Muneef ne daga shi sai karamin towel ko cinyoyinsa bai rufe ba,dawani a hannun sa yana goge jikinsa tana ganin shi a haka tayi sauri ta juya
Cikin sauri ya capkota.................




















_Beebah wadata_
 4 comment
+2349061540805
Beebahwadata.Blogspot.com

Comments

Popular posts from this blog

NA TSANI AURE 1 to 10

NA TSANI AURE 11 to 20

NA TSANI AURE 21 to 30