BAN YI TUNANI BA 31 to 35

••••••••••❤❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤••••••••••
••••••••••❤••••••••••

*BAN YI TUNANI BA*

® *{P M L W}*
_pure moment of life writers_
```(we don't just entertain and educate we also touch the hearts of the readers)```

*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

Beebahwadata.blogspot.com

     *Written by*
```Beebah wadata```

_wannan shafin naki ne *ummieyn bayan layi* Enx 4 d luv n kia ILYSM_

*31 to 35*

Da kanshi ya bud'e mata motarta ta shiga,shima ya shiga tasa,sai da ya raka ta har ta shiga gate din gidanta saanan ya juya ya tafi,falo ta wuce inda ta bar handouts nata nan ta gansu,karatu ta fara bata gama ba sai kusan one o'clock, ganin lokaci yasa tayi sauri ta tashi,wanka tayi ta d'auro alwala,tea ta had'a ta sha saanan ta dauk'e akwatu nan ta ta saka bayan mota,direct Dan fodio ta nufa,daga gidanta akwai nisa,
sai da tayi 20min tana tafiya,koda Isar ta su Bafnah sun fara shiga layi,layin tayi joining tashi

Bayan sun fito ne suka had'u da Amra

"Aaaaaa Amarya mai kamshin lalle,har kin fara fita kenan" Amra tayi maganar tana murmushi

"Ba dole ba test ya fito da ni"

"Ya angon naki,yana laipa koh"

"Eh lapia lau" ta bata amsa a takaice

"Bafna ya dai naga kinyi shiru,ko duk test d'in ce?" Amra ta tambaye ta

"Bakomai kawai dai,mind d'ina tana wani gurin"

"uhmm.ko dai tunanin Doctor d'inki ki ke?" Husnah ta tambaye

"Bawani tunanin shi da nake,kuma ai kona yi laifi ba" ta murgud'a musu baki

Husnah tace "Lallai kin zare,kin zama lover girl"

Bafna tace "Ba dole ba zama da ku,ai dole na zare"

"To da sa'uran ki dai ki jira kiyi aure". Husnah ta fad'a

Dariya Bafna tayi sa'anan tace "Haba ke da muka kai shikeranjiya zaki cemin kin wani san aure,bar'i Amra ta fad'a haka ita da ta kwana biyu".

Amra ta katse zanc'en da cewa " kun ga ku tashi muje central mosque,idan na biy'e ta ku sai mu kwana ana zanc'en"

Duba Husnah tayi a parking space bata ga motar Amra ba "Amra ina motarki?".

"Ba da mota nazo ba Baba Sudais ya hanani,wai nayi nauyi sosai ko sudais dazu wurin Umma muka kaishi"

"Da gaskiyar shi,ni yanzu Husnah kawai nake son nagani da ciki wallahi" Bafna tayi magana cikin tsokana

"Ke Bafna jan maganar ki yayi yawa"

"Husnah tace kyaleta ni take son nayi magana kuma bazan yi bah"

Motar Husnah suka shiga,central mosque suka wuce can sukayi sallah suka tab'a fira

"Uhm Ku tashi muje yau old airport zan wuce,gidan aunty Muneef,baya garin can zan zauna har ya dawo"

"Allah ya dawo da shi tafiya" Amra tace

"Ameen,ni da ke duk na all thesama" Bafna ta fad'a tana nuna Husnah

"Naji dai koma minene muje kawai"

Skul din suka fita,Kangiwa road akayi dropping din Bafna, sa'anan ta a'jiye Amra Arikillah,Ku da ta Isa gidan Aunty balkisu 6 tayi,parking tayi ta fiddo akwatu nanta mai gadi ta kira ya taimaka mata ta shiga dasu,Aunty na zaune a falo

"Sannu da zuwa,Ashe kina tafiye?,yanzu nake da niyyar kiranki naji"

Murmushi tayi sa'anan tace "Eh skul naje shi yasa baku ganni tun dazu ba"

"Allah sarki wani Abu Ku kayi a skul d'in ne?". Aunty billy ta tambaye ta

" test muka yi,bamu San da ita ba k'watsam muka ji ta"

"Allah yasa anyi a sa'a kenan"

"Ameen..... Wai ina Hunaida ne?".

"Tana gidan su Mamiey,gidan kusa da mu,bari na kira Ladi(Ita ce mai aikin gidan) ta taya ki kai kayan ki d'aki"

Ladi ta k'walawa kira cikin ya dak'ika kad'an tazo..........







_Beebah wadata_

Comments

Popular posts from this blog

NA TSANI AURE 1 to 10

NA TSANI AURE 11 to 20

NA TSANI AURE 21 to 30