BAN YI TUNANI BA 36 to 40

••••••••••❤❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤••••••••••
••••••••••❤••••••••••

*BAN YI TUNANI BA*

® *{P M L W}*
_pure moment of life writers_
```(we don't just entertain and educate we also touch the hearts of the readers)```

*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

Beebahwadata.blogspot.com

     *Written by*
```Beebah wadata```

_Wannan shafin naku ne masoyan wannan littafi na Fb ina jin dadin comments dinku...Allah ya bar kauna_

*36 to 40*

"Hajiya gani" Ta d'an durk'usa

"Ga matar Muneef  fa" ta fad'a tana nuni da Husnah

Washe hak'ora tayi "Aunty ina wuni"

"Lapia lau y aiki?"

"Angode Allah" Ladi ta fad'a

Kayan ta taimaka mata ta shiga dasu ciki,gadon ta zube ta lumshe ido,bud'e kofar da akayi tasa ta bud'e ido Hunaida  ce da gudu ta hawo gadon

"Aunty yaushe kika zo?,kinyi wanka?,kin ci abinci?".

"Kai Hunee duk wannan tambayoyin ni d'aya"

"Eh mana,kinsan yanzu nine uncle". Ta nuna kanta

Dariya Husnah tayi " owk oga Muneef "

 kyalkyale suka yi da dariya

"Shine kika k'i cewa mami a d'akina zaki zauna fushi ma nake da ke"tayi maganar ta zunburo baki

Hannunta ta rik'e "Yi  hakuri,mai kyau d'iyar Maminta,na d'auka d'akinki  ki za'a kawo ni,sai kawai naga an shigo da ni nan"

"Kai aunty harda su bada hakuri ai ya wuce,yanzu bari naje nayi wanka"

"Kece ogan ai shiyasa"
Dariya sukayi su duka

_*1 week later*_
    Jamil yana kula da ita kamar yadda yayi wa Muneef alkawari

     A bangaren Muneef yana gudanar da aikin sa yadda ya kamata,Da ya samu free time zai kira Husnah su sha wayar su

  "Hunaida Auntynki ta dawo skul?" Aunty balkisu ta tambaye Hunaida da ke zaune kusa da ita tana buga game a waya

"Aa bata dawo ba amma dai nasan tana kan hanya...."
Sallamar ta da suka ji ita ta katse musu zance

"Y'ar halak kin ki ambato,yanzu muke maganar ki" Hunaida da Fad'a

Zama tayi ta gaida Aunty Bilkisu

"Yawwa Husnah gobe Babansu Hunaida zai dawo tare da khaleed".

"Allah ya kawo su lapiya bari mu fara shirye shirye kenan" Husnah ta fad'a fuskarta d'auke ta farin ciki

"Baki ga Mami ba bakin ta ya kasa ruf'ewa Dady zai dawo" Hunaida tayi maganar ta kallon Aunty Bilkisu

"Gidan Ku yanzu har da ni baki bari ba ko,kin girm........"

Hunaida ta yi saurin cewa
"Allah ya huc'e  zuciyar ki uwata"
Dariya sukayi su duka

Washegari tun da safe suka fara aiki abinci sunyi kaloli ya kai kala biyar,sai 2 suka natsuwa,kowa ya nuf'e dak'inshi don yin wanka

K'arfe hud'u suka Khaleed suka iso gidan,Aunty Bilkisu da ita Husnah dake falo zuka ji horn a aguje sukayi waje

"Oyoyo ya khaleed" Hunaida ta fad'a tare da hugging nasa

"Kai sweet sis kinga yadda kikayi kyau" Khaleed yayi magana tare da rik'e hanc'in ta

"Ni sake min hanc'in daga dawowa sai mugunta" tayi maganar tana turo baki

Aunty Bilkisu kam ta mak'ale da mijin ta sannu kawai take masa,kamar Wanda akace yayi ciwo

"Dady sannun da zuwa" Hunaida tayi hugging nasa

"Aa bana so sai yanzu kika gani"

"Lahhh..yi hakuri dady kawai na Dad'e ban ga yaya bane

"Son ya hanya?"
"Alhamdulillah Mami,mun same ku lapia"
"Lapia lau"

Falo suka nufa hira suka fara yi ganin hirar ba ta k'arewa  ba ce yasa ta ja mijinta sukayi gaba

"Sis bari naje nayi wanka" ya mik'e ya shiga ciki

Direct dak'unan ya nufa,Yana bude dak'insa....macce ya hango kwance akan gadon sa, A hankali ya fara taku har ya isa wurin,gashin da ya rufe fuskarta ya janye, gabansa ne ya fadi lokacin da yayi arba da k'yak'yawar fuskar ta,jikin ta ya biye da kallo har ya sauke idon sa akan kirjin ta.....

Toh pha wacce wannan budurwar?




Muje zuwa
             Iya wuya ana tare





*Beebah wadata*
 4 comment
09061540805

Comments

Popular posts from this blog

NA TSANI AURE 1 to 10

NA TSANI AURE 11 to 20

NA TSANI AURE 21 to 30