BAN YI TUNANI BA 41 to 45

••••••••••❤❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤••••••••••
••••••••••❤••••••••••


*BAN YI TUNANI BA*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
```(we don't just entertain and educate we also touch the hearts of the readers)```

*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

Beebahwadata.blogspot.com


     *Written by*
```Beebah wadata```



*41 to 45*


Jikin ta yabi da kallo har ya sauke idon sa akan kirjin ta hannu ya kai zai tab'a ta komai ya tuna kuma sai ya janye, Falo ya dawo inda ya bar Hunaida nan ya taddo ta wayarta a hannunta sai game take,wayar ya warce


"Haba Yaya miye haka ka bani Dan Allah kar su cinyeni". Tayi maganar kamar zatayi kuka


"Hhhhh....Au wai kuka zaki to yi kukan nagani,dama na dad'e banga kukan ki ba" Yayi Fad'a cikin sigar tsokana


"Ni dai ka bani kawai plx, To wai miye ya fito dakai kai da kace min zaka yi wanka?".


"kin ga d'akina na kasa ganewa".


"Oh! Sorry laifina ne na manta an chanza ma d'aki,wannan d'akin na farko".


"Wai wa ma yace a chanza min ne?".


"Oho nima bansani ba kaje ka tambaye Mami mana ai wannan maganarku ce". Ta Fad'a tana turo baki


Wayar ta ya tillo mata ya nuf'e d'akin da aka ce nasa, Sosai d'akin ya burge sa komai na ciki white ne,toilet kawai ya wuce cikin y'an mintuna da basu wuce ashirin ba,Ruwan da nagani a jikinsa saanan d'aure yake da towel su suka tabbata min wanka yayi Jikinsa ya tsane,Bai wani dau lokaci ba sai gashi ya fito sak dashi cikin Jeans da T-shirts,Tsohon d'akinsa ya nufa haka kawai ya tsince kansa da son k'ara ganin wannan yarinyar daxu da ya gani d'akin sa, A hankali ya tura kofa,sai dai mi wayam bai ga kowa ba kuma an k'ara gyara d'akin,Falo ya nufo wata irin murya yake jiyo tana dariya daga falo,Da sauri ya k'arasa ciki,Wannan yarinyar ya hango
Sai dariya suke ita da Hunaida, kujerar da ke kusa da su ya zauna,d'ago kai Husnah tayi ta kalle shi ku ba'a Fad'a mata ba wannan shine Yayan Hunaida


A d'an sanyaye tace "Ina wuni,Ya hanya?".


Kafin ya amsa su Dady suka fito fuskar su d'auke murmushi


"Ina Wuni,Ya hanya?". Husnah ta cewa Dady


" Lapiya lau,Wannan itace Husnah ko Hajiya?". Ya tambaye Aunty bilki


"Eh ita ce,Matar dan auta".


Khaleed yace "Wai dama Mami Wannan ita ce matar Ya Muneef ".



"Eh,itace Husnah ga khaleed, Khaleed ga Husnah". Tayi ta Fad'a tana nuna su da hannu


"Wow amma uncle ya iya zab'in mata". ya fad'a ya satar kallon Husnah


Hunaida kam game kawai take yi sai da dady ya karb'a wayar saanan tace abin, Khaleed sai satar kallon Husnah yayin da ita ko duk ta takura jira kawai ta ga Hunaida ta tashi itama ta bita, Amma ta ki ta tashi, A haka dai suka kammala koya ya tashi,Husnah direct d'akin da take ta nufa wayarta ta d'auko ta kira Muneef sun dad'e suna waya da bisani suka yi sallama


*******
A bangaren Khaleed ya na fita gidansu abokinsa ya nufa Safwan, Horn yayi mai gadi yaxo zai bud'e sai ga shima ya fito, Fitowa suka yi su duka tafawa sukayi irin na samari



Safwan yace "Badguy saukar yaushe?"


"Daxu na dawo wallahi, Hope mun sameku lapia?''.



"Lapiya lau, Amma shine baza'a ko gaya mamu ba". Safwan yayi maganar wai shi dole yayi fushi



"Haba sowrie frnd, Surprise na ke son na baka".



"Ummm...toh naji amma nasan ka sanarwa Sophie ko?".



"Aa ban sanar mata ba, So nake kawai ta ganni a kofar gidan su".



"Haba Man ai da ka gaya mata da ta dan gyara jikin mana".



"Hmm...ai kasan ni kada'i CE da ita,Bata min sharing,Ka maida motar muje da tawa kawai". Khaleed ya fad'a lokacin da yake kokarin shiga motarsa


Hanyar gidansu Sophie suka nufa...........






Iya wuya ana tare🤝





_Beebah Wadata_

Comments

Popular posts from this blog

NA TSANI AURE 1 to 10

NA TSANI AURE 11 to 20

NA TSANI AURE 21 to 30