BAN YI TUNANI BA 61 to 65

••••••••••❤❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤❤••••••••••
••••••••••❤❤••••••••••
••••••••••❤••••••••••

*BAN YI TUNANI BA*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
```(we don't just entertain and educate we also touch the hearts of the readers)```

*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

Beebahwadata.blogspot.com

     *Written by*
```Beebah wadata```


_wannan shafin naki ne Namcy *Bieboh* Ina ji dake sosai  ILYSM 😍_



*61 to 65*



Khaleed da Husnah take kwance a kirjinsa sai magiya yake mata, Su kara another around Amma taki, Wayar sa ta fara ringing, Amma Sam hankalinsa baya kanta, Wani kirane ya k'ara shigowa k'aro na biyu



"Wai baka jin ana kiran ka ne". Sophie ta fada lokacin da take tureshi a jikinta



Janyo ta yayi ya rungume yana shafa bayanta "Ki bar ta kawai yanzu haka Safwan ne so yake ya takura ni.



Wani kiran ne ya sake shigowa k'aro na uku tsaki yayi ya janyo wayar "Amma wlh sai na ci uban Safwa......". Sunan da ya gani a screen din wayar sa yayi saurin mikewa zauna, Ya ture Sophie gefe daya




"Hlo Dady" ya Fad'a cikin girmamawa har da su runsunawa tamkar yana ganinsa



"Kaina ina ne tin daxu nake kiranka kaki kayi picking"



"Oh ...Sorry Dady na saka wayar a falon Safwan mu kuma muna bedroom nasa kuma wayar silent take".



"Toh kayi sauri ka dawo gida kafin takwas da rabi, Kasan bana son yawo koh".



"Allah ya huce zuciyarka gani nan zuwa". Saanan sukayi hanging call d'in.



Sophie dake zaune gefensa gani kawai tayi yana maida kayan jikinsa
Tace "Ya dai, Naga kayana maida kayan jikinka ko ka  hakura ne?".



"Zaki tashi na Kai ki gida ne, Kuma nayi wuce wana". Ya Fad'a lokacin yake girma zaman belt dinsa



Cikin mitunan da ba zasu wuce biyar ba suka shirya tsaf, Cikin mota ma ba mai magana Khaleed sai duba agogo yake yi, Nesa daga gidansu Sophie yayi packing



"Ba zaka k'arasa dani kofar gida bane?".


" Eh" kawai yace mata



"Amma gobe ma zaka dawo ko?". Tayi maganar tana murmushi had'e da  kallon fuskarsa, Ganin da tayi ya had'e rai ne yasa ta sha jinin jikinta



"Dillah zaki fitar a mota ko sai na fitar da ke ne". Ya k'arasa maganar tare da buga wani wawan tsaki



Fau ta fita daga motar lallai ma wannan mutumin ya raina min da wayo Amma zan yi masa Hankali, Umma da ke bakin gate ta fito mak'wabta wurin barka, A idonta taga fitowar Sophie a cikin mota, Saurin shiga gidan tayi a falo ta zauna tana jiran shigowar ta



Baa fi minti uku sai gashi ta shigo rai b'ace ko sallama ma batayi ba,har zata bi hanyar da zata sada ta da d'akin ta yaji ance



"Ke....Daga gidan ubanwa kike a daren nan"



Tsayawa tayi cak don batayi zaton Umma na falon ba



"Magana nake miki kin wani jiyo kin tsareni da ido".


Ganin da tayi fuska umma ba wasa a tattare da ita yasa ta dawowa ta zauna kasa kusa da umma



"Umma gidan su Siyama naje shine yayanta yace bari yayi dropping dina gidd...."



Tas,kake ji Umma ta wanke Sophie da mare
"Yanzu Safiyya rayuwar da kika daukarwa kanki tayi dai dai, Mi kika rasa CI ko sha ko sutura, Ko kina tinani duk abinda kike yi baya dawo min dan kings na saka miki ido shiyasa zaki lalace koh?".



Cikin kuka Sophie tace "Ni fa Umma ba abinda nake yi kuma duk Wanda ya Fad'a miki yayi min karya wallah....."



"Yi min shiru mutuniyar banza, Ke na gane sam baki da hankali, Har ynx rud'en duniya bai sake ki ba, Shin ina kika kai ilimin ki, Tunanin duk ina suke, Idan ni kina boyemin abinda kike kina tsoron kar naji shin bakya tsoron ranar da zaki tsaya a gaban ubangijin ki, Lokacin gab'ub'in jikin ki zasu ba da shaida ranar da duk abinda ka boye zaaji, Ai da kunyar lahira kwanda ta duniya, Safiyya ke macce haka zai iyayi miki illa bama ke kadai ba har da lyalinki nan gaba, ina tsoron ranar da asirin ku zai tuno keda Dadynki, Duniya tasan ko ku suwaye, ki ji tsoron Allah ki tuba zama na kirki she Ke da wuya, Allah yasa mu dace tashi ki tafi" Umma ta k'arashe maganar cikin muryar kuka zaninta ta jawo ta goge kwallar ta ta zubo mata



"Umma Dan Allah kiyi hakuri na tuba bazan k'ara ba, Wat a shame ace ni nasaka mahaifiyata kuka akaina, Dan Allah ki yafe min". Ta Fada jikin Umma tana kuka



"Ni na yafe miki, Zan CI gaba da ya miki addua,tashi kije ki kwanta kinga Tara ta wuce".



Tashi tayi ta wuce ciki, Alhaji Aminu (Dadyn Sophie) da tin daxu ya dawo yana tsaye a bakin falo yana sauraren abinda Zulfa'u (Umma) take Fad'a ma Sophie sosai jikinsa yayi laasar don shi bai tab'a zaton Sophie tana harka da maza, Shi da yake bata wasu shima Ashe an bata masa tasa kwallar da ta zubo masa ya goge...................😢








Muje zuwa
_Beebah wadata_

Comments

Popular posts from this blog

NA TSANI AURE 1 to 10

NA TSANI AURE 11 to 20

NA TSANI AURE 21 to 30